Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin kama dukkan wata kungiya da aka samu ta na tallafawa ko kuma kare hakkin masu auren Jinsi a Jihar.

Gwamnatin karkashin jagirancin Jihar injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bai’wa hukumar hisba umarnin kawo karshen duk wata kungiya da ke tallafawa auren Jinsi a Jihar.
Hadimin gwamnan kan yada labarai Abdullahi I Ibrahim ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X.

Sanarwar ta ce tallafawa ko kare hakkin masu auren jinsi ta hanyar bayyanawa a fili ya sabawa dokar Jihar.

Gwamnatin ta dauki matakin hakan ne bayan gano wata kungiya da tayi mai suna WUSE da ke tallafawa da kuma rajin kare masu auren jinsi a Jihar.