Jami’an Operation Haɗin Kai sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram 12 a wani hari da suka kai musu a kusa da dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jami’an sun farwa mayakan ne a jiya Juma’a.

Zagazola ya ce jami’an Operation Hadin Kai na Desert Sanity III, dana Hybrid Force ne suka farwa ‘yan ta’addan a yankunan Bula Dalo, Bula Marwa, Gaizuwa, da Chongolo da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bama a Jihar ta Borno.

Wasu majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa kwantan ɓaunar da jami’an suka yiwa ‘yan ta’addan ya sanya suka tsere daga yankin.

Majiyar ta kuma ce an samu jami’an tsaron sun kashe ‘yan ta’addan 12, inda suka ƙwato wata nakiya IED guda ɗaya tare da bindigogi kirar AK-47 guda uku, keke ɗaya, da tutocin guda uku, da kuma wasu magunguna.

Har ila yau sojin sun ceto wasu mutane 16 da ke hannun maharan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: