Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane 21 da ke satar danyen mai a yankin Neja Delta.

 

Bayan kama mutanen an lalata haramtattun matatun mai guda 43.

 

Mai rikon mukamin jami’in hulda da jama’a na rundunar Latanal Kanal Danjuma Jinah Danjuma ne ya bayyana haka a Bayelsa.

 

Ya ce jami’an sun samu nasara n hadin guiwa da da sauran jami’an tsaro.

 

A cewarsa, an kama bututun mai guda 12 a yankin Ojobo da ke karamar hukumar Ekeremor.

 

Sannan sun kama mai da aka sata mai yawa.

 

Kakakin ya ce an lalata haramtattun matatun mai guda 43 a harin da su ka ƙaddamar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: