Shugaban Kasa Bola Tinubu na shirye-shiryen tafiya Kasar China Kwanaki kadan bayan dawowarsa daga Kasar Faransa.

Mai magana da yawun shugaban Ajure Ngelela ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Ngelale ya bayyana cewa shugaban zai tafi kasar ta China ne a farkon mako mai kamawa na watan Satumba.

Mai magana da yawun shugaban ya ce ziyarar ta Tinubu na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatinsa ta ke yi na inganta rayuwar ‘yan Kasar.

A ziyarar ta Shugaban ana sa ran zai gana da Shugaban Kasar ta China Xi Jinping, domin sanya hannu akan wasu yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Tinubu zai kuma gana da shugabannin wasu manyan kamfanoni guda 10 na ƙasar China da suka shafi albarkatun mai da iskar gas, da kuma samar da aluminium, da harkar noma, da kuma fasahar tauraron ɗan adam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: