Kamfanin mai na Kasa NNPCL ya bayyana cewa ya fara fitar da iskar gas zuwa Kasashen China da Japan ta jiragen ruwa domin sayarwa.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin OIufemi Soneye ya fitar a jiya Litinin.

Soneye ya bayyana cewa shugaban kamfanin ta ce mai na kamfanin na NNPC Segun Dapo, ya ce fara fitar da iskar gas din, na daga cikin shirye-shiryen kamfanin na samar da ingantaccen makamashi a kasuwannin duniya.

Sanarwar ta ce bangaren fitar da iskar gas din ya samu gagarumin hadin kai daga bagarorin kamfanin NNPC na gas da kuma na sufurin jiragen ruwa.

Sanarwar ta ce tun a ranar 27 ga watan Yuni 2024 jirgin farko dauke da iskar ta gas din ya bar Najeriya zuwa Kasar Japan.

Soneye kara da cewa a shekarar 2021 da ta gabata kamfanin na NNPC ya fara kasuwancin gas, kuma kawo yanzu ya fitar da jirager ruwa sama da 20 na gas zuwa yankunan Asiya da kuma turai.

Har ila yau kakakin kamfanin ya ce, Dapo ya ce fitar da iskar gas din hakan zai bai’wa kamfanin damar kara karfafa harkokinsa domin samun kaso mafi yawa a bangaren ta yadda zai kara daukaka da harkar iskar gas.

Sanarwar ta tabbatar da cewa nan da watan Nuwamba shekarar nan, ake sa ran kamfanin na NNPC zai aike da jirage fiye da biyu na gas zuwa kasuwannin kasahen duniya har zuwa karshen shekarar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: