Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya bayyana cewa tun a zamanin tsohon gwamnan Jihar Aminu Waziri Tabuwal aka samu nakasu a yaki da ‘yan ta’adda a Jihar, ya yin da a halin yanzu yake kokarin shawo kan matsalar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin babban mataimakinsa na Musamman kan kafafen sada zumuta Nasir Bazza ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.
Sanarwar ta ce a lokacin tsohon gwamnan Jihar Tambuwal jami’an tsaron soji ba su samu wata nasara ba, a yaki da suke yi da ‘yan ta’adda a Jihar ba sakamakon ba su da wani karfin da za su iya kai hare-hare a lokaci daya a dukkanin kananan hukumomin da ke fadin jihar.

Bazza ya kara da cewa da tsohon gwamna ya kafa ya kafa rundunar tsaron sa-kai a lokacin mulkinsa, to babu shakka da gwamnati mai ci a yanzu ta dora daga inda ya tsaya.

Kazalika Bazza ya bayyana cewa babu wata gwamnati da take biyan kudin fansar mutum bayan, yin garkuwa dashi, ko kuma yi sulhu da ‘yan ta’addan.
Acewarsa biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga ko yin sulhu da su hakan zai haifar da wata babban matsala ga gwamnatin wadda za ta gaza shawo kan ta.
Har ila yau Bazza ya ce da a ce gwamnatin Jihar ta Sokoto ta biya kudin fansar Sarkin Gobir da aka yi garkuwa dashi, da zuwa karshen shekara gwamnatin ta biya biliyoyin kudade a matsayin kudin fansar mutanen da aka sace.
Nasir Bazza ya ce biyan kudin fansar hakan zai sanya ‘yan bindigar sun yi amfani da kudaden wajen ci gaba da siyo makamai, kuma su ci gaba da rike mutanen da ka biya kudin fansar ta su.