Tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa salon yadda shugaba Tinubu ya ke tafiyar da gwamnatinsa tamkar motace a tsakiyar daji babu direba.
Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a yau Laraba.
Atiku ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Tinubu ba ta san inda ta sanya gaba ba tun bayan hawanta kan karagar mulkin kasar.
Atiku na wannan kalamin ne bayan da gwamnatin ta bijiro da wani sabon tsarin da zai haramtawa dalibai ‘yan kasa da shekaru 18 rubuta jarrabawar kammala sakandire a Kasar.
Tsohon mataimakin ya ce matakin na gwamnatin ta Tinubu, tamkar matukin jirgin ruwa ne da ya bace a cikin tsakiyar Teku.
Acewar Atiku haramtawa ‘yan kasa da shekaru 18, rubuta jarrabawar kammala sakandire, hakan babban nakasu ne a harkar neman ilmi, da kuma koma baya.
Kazalika ya ce gwamnatin ta Tinubu ta sanya ilimin Kasar a tsarin ayyukan yau da kullum wadda gwamnatocin jihohi ke da karfin iko a kai sama da ta gwamnatin Tarayya.
Atiku ya ce ya kamata ‘yan kasar su fito su kalubalanci kudurin gwamnatin, wanda ya kira shi da mulkin kama karya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: