Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na lll ya nada gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris a sarautar gwarzon daular Usmaniyya.

 

Wakilin Sarkin Musulmi kuma sarkin Argungun Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya mika takardar nadin ga gwamnan a gidan gwamnatin Jihar ta Kebbi a jiya Juma’a.

 

Alhaji Sa’ad ya nada gwamna Nasir ne a sarautar ta Gwarzon Daular Usmaniyya ne bisa gudummuwar da yake bayarwa na taimakon al’ummar kasar.

 

Sarkin Muslumin ya bayyana cewa sarautar gwarzon daular Usmaniyya ana bayar da ita ne ga dukkan wanda ya sadaukar da kansa wajen taimakon al’ummar Jiharsa da dama Kasarsa baki daya.

 

Sarkin na Argungu ya kara da cewa masarautar Sarkin Musulmi na sa ne da irin gudummawa taimako da kuma kyautatawar da gwamnan ya ke bayarwa a wajen inganta rayuwar al’umma.

 

Acewar Argungun Majalisar masarautar sarkin Musulmi za ta bayyana ranar da za ta nadawa gwamnan rawanin sarautar nan ba da dadewa ba.

 

A yayin karbar takardar nadin gwamna Nasir ya mika godiyarsa ga masarautar sarkin Musulmi bisa dacewar da ta gani ta nadashi a matsayin.

 

Sannan gwamna Nasir ya ce gwamnatinsa da mutanen Jihar za su samar da lokaci domin zuwa yin godiya fadar Sarkin Musulmin da ke Jihar Sokoto domin nuna farin cikinsu da nadin da aka yi masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: