Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta ƙasa FRSC ta bayyana cewa, mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani haɗarin mota da ya afku ranar Alhamis, a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke Hotoro a Kano.

Ta kuma sanar da cewa, akwai ƙarin mutane 48 da su ka samu mabanbantan raunuka, a cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Kwamandan rundunar ta FRSC a jihar Kano Umar Matazu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani jawabi da aka fitar jiya Juma’a.

Ya kuma ƙara da cewa iftila’in ya rutsa ya faru ne da wata babbar motar dakon kaya, wacce ta ke ciƙe maƙare da kayayyaki da kuma fasinjoji.
Kuma hatsarin ya rutsa ne da mutane 71, waɗanda 67 daga cikinsu manya ne, sai kuma ƙananan yara guda huɗu, inda tun a lokacin da lamarin ya auku, aka garzaya da waɗanda su ka samu raunuka zuwa babban asibitin Murtala Muhammad dan basu agajin gaggawa.
Matazu ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa, matuƙin motar ya kasa sarrafa ta ne sakamon tsananin gudu da ya ke yi, wanda hakan ne musabbabin faruwar haɗarin.
Ya kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukansu tare da jajantawa waɗanda su ka samu raunuka, inda a ƙarshe ya gargaɗi matuƙa ababen hawa da su gujewa ɗibar kaya da kuma fasinjoji a lokaci guda, dan kiyaye afkuwar haɗurra.