Gwamnatin tarayyar Najeriya ta miƙa kuɗi kimanin Dala dubu 132, 364 da kuma Naira miliyan 78, 566, 324 da aka karɓo daga ƴan damfara, ga ƙasashen Amurka, Sifaniya da Swaziland.

Dukka wannan dai a ƙoƙarinta ne na yaƙi da kuma daƙile cin hanci da rashawa, da kuma biyan diyyah ga waɗanda aikin ƴan damfarar ya shafa.

Shirin miƙa kuɗin dai ya gudana ne ƙarƙashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, wacce ayyukanta ne su ka gano kuɗaɗen da sauran kayayyaki daga ƙananan ƴan damfarar a faɗin ƙasar.

Taron wanda ya gudana a shalkwatar ta EFCC da ke Jabi a birnin tarayya Abuja, ta samar da kuma ɗaga ƙimar Najeriya a idanun ƙasashen ƙetare.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale, da ya ke magana a yayin taron shugaban hukumar Ola Olukoyede, ya bayyana farin cikinsa game da taron.

Ya kuma bayyana cewa wannan ƙoƙari ne na wanzar da kyakkyawan shugabanci, da kuma saisaita tattalin arziki da tabbatarwa da duniya cewa Najeriya ba matserar masu aikata laifi ba ce.

Abubuwan da aka miƙa ga wakilan ƙasashen bayan tsabar kuɗi, akwai ababan hawa da kuma gidaje ga ƴan ƙasashen na Sifaniya, Amurka da kuma Swaziland.

Wakilan da su ka karɓi kayayyakin sun haɗar da Ambasadan ƙasar Sifaniya a Najeriya Maria Higon Velasco, babban jami’i daga ofishin jakadancin ƙasar Swaziland a Najeriya Florent Geel da kuma jami’in hukumar binciken sirri na ƙasar Amurka Charles Smith.

Leave a Reply

%d bloggers like this: