Shugaba Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeeriya da su ci gaba da haƙuri bisa matakan da gwamnatinsa ke dauka don samar da ci gaba a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaba Tinubu kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Jiya Juma’a.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Limaman Mabiya addinin kirista na Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria a Fadarsa da ke Abuja.

Shugaban ya bayyana cewa duk da cewa gwamnatinsa ta kasance mai jin koken Mutane ce, amma ya na bukatar a ci gaba da hakuri nan bada jimawa ba sauki na tafe.

Shugaban ya ce ya dauki matakai masu tsauri ne bayan karbar ragamar Kasar a shekarar 2023, kuma daga ciki har da matakin cire tallafin man fetur.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa duk da daukar matakai masu tsauri da gwamnatinsa ta yi alamu na nuna cewa sauki da nasara na nan zuwa.

Acewarsa daminar da ta gabata ta yi albarka sosai duba da cewa farashin kayan abinci na sauka, inda kuma farashin man fetur shi ma na sauka.

Sannan shugaban ya tabo batun matsalar rashin tsaron da ta addabi Kasar nan, ya ce Matsalar ta shafi musulmi da kirista ne, yana mai cewa uwargidansa kirista ce don haka zai goyi bayan dukkan al’amuransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: