Kwamitin ladabtarwa na Majaaisar Dattawa ya bukaci shugaban Majalisar Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti da su bayyana a gabansa don fara gudanar da bincike kan zargin da Sanata Natasha ke yiwa Akpabio na cin zarafinta.

Mataimakin shugaban Kwamitin Sanata Onyekachi Nwebonyi ne ya bayyana hakan ta hirarsa da Chamnels Tv a jiya Juma’a.
Onyekachi ya bayyana cewa Natasha da Akpabio za su bayyana a gaban Kwamitin, sannan za a saurari shaidun kowanne bangare.

Ya ce Kwamitin zai kuma dauki bayanansu, tare da saurarar sauran Sanatoci, don ganin an yiwa kowanne bangare adalci.
