Cibiyar ƙididdiga ta ƙasa NBS ta fitar da rahoton hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, na watan Fabarairun shekarar 2025 da mu ke ciki.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 23.18 cikin 100 a watan Fabarairun, daga kashi 24.48 cikin 100 na watan Janairu.

Rahoton ya ci gaba da cewa, a matakin shekara-shekara na watan Fabarairun 2025, hauhawar farashin a birane shi ne kashi 25.15 cikin 100, wanda hakan ke nuna ya ragu da kashi 8.1 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 33.66 cikin 100 na watan Fabarairun shekarar 2024.

Rahotan ya kuma bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a yankunan karkara kuwa ya kasance kashi 19.89 cikin 100 a watan na Fabarairu, hakan ya nuna ya ragu da kashi 10. 09 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 29.99 cikin 100 na watan Fabarairun shekarar 2024.

Hukumar ƙididdigar ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyakin ya ragu, duk kuwa da ci gaba da ƙorafin tsanani da tsadar rayuwa da al’umma su ke yi a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: