Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC ta gurfanar da babban Akanta janar na Jihar Bauchi Sirajo Muhammad Jaja a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zarginsa da yin almundahanar naira biliyan 8.3.

EFCC ta gufanar da Jaja ne a jiya Litinin, tare da wani mutum mai suna Aliyu Abubakar da ke sana’ar canji, da kuma wani kamfani mai suna Jasfad Resources Enterprise.

Hukumar ta bayyana cewa ta gurfanar da mutanen a gaban kotun ne bisa zarge-zarge Tara da take yi musu, wadanda suka shafi halasta kudin haram, da kuma laifin almundana da dukiyar mutane.

Sannan kuma hukumar na zarginsu da yin sama da fadi da kudin gwamnatin Jihar Bauchi, da kuma karkatar da kudin da ya kai sama da naira biliyan 8.

Hukumar ta ce tana kuma zargin Tsohon Sakataren gwamnatin Jihar ta Bauchi Ibrahim Kashim, Sakataren gwamnatin Jihar na yanzu da hannun a cikin lamarin.

EFCC ta ce sauran sun hada da Balarabe Abdullahi, Saleh Muhammad, inda suka tserewa kamun hukumar.

Bayan gurfanar da wadanda hukumar ta ce zargi a gaban kotu sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: