Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate ya ce fiye da likitocin Najeriya dubu 16,000 ne suka yi hijira daga kasar zuwa kasashen Ketare.

Ministan ya bayyana hakan ne a jiya Talata a gurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin yankin Afrika a birnin Tarayya Abuja.
Pate ya ce wadannan likitoci sun bar gida Najeriya ne zuwa sassan Duniya a cikin shekaru Biyar zuwa Bakwai, don gudanar da ayyukansu a cikin yannayi mai kyau.

Acewar Ministan har yanzu ana kara samu wani adadi mai yawa na likitoci masu kwarewa, da ke da niyyar tafiya Kasashen ketare don yin aiki, sakamakon fakewa da suke yi da rashin kyawun yanayin aiki da kuma matsalolin tattalin arziki, da kuma samun cikakken horo, bayan yin zuzzurfn bincike akan Kasashen.

Pate ya kara da cewa ba sabon abu ba ne hijirar kwararrun likitoci daga Kananan Kasashe zuwa Kasashen da suka ci gaba ba, yana mai cewa sai dai adadinsu na kara karuwa a ‘yan shekarun bayan nan.
Kazalika Ministan ya nuna rashin jindadinsa bisa yadda nas-nas da ungozomomi a Najeriya ke tafiya zuwa ketare, ya ce hakan na kara rage adadin Ma’aikatan lafiya da ake da su a Kasar nan.
Har ila yau Pate ya ce alkaluma sun nuna akalla likitoci hudu ne ke duba mutane dubu Goma a Kasar nan, yana mai kiddige cewa fiye da Dala dubu 21 a matsayin kuɗin da ake kashewa kowanne likita daya wajen bashi horo.