Gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya nada shugabannin kananan hukumomi 23 na fadin Jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar Ibibia Lucky Worika ya fitar a yau Laraba a Fatakwal babban birnin Jihar.

Sanarwar ta ce gwamnan rikon ya kuma amince da canja dukkan majalisun gudanarwa na Cibiyoyi, ma’aikatu, da kuma hukumomin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu.

Acewar Sanarwar nadin wadanda za su jagoranci ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: