Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna sun kai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Kaduna.

A ziyarar akwai tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu manyan ƴan siyasa.

A wani bidiyo da Atiku ya wallafa, an hango su su na taha da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A gefe guda kuwa wasu na tunanin ko hakan na da alaƙa da zargin yiwuwar dunƙulewa waje guda don kwace mulki daga jam’iyya APC.

A kwanakin baya an jiyo Atiku na bayanin yiwuwar hadewar manyan yan siyasar waje guda don karɓe mulkin ƙasar daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakan kuma na zuwa ne kwanaki kaɗan da tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufai ya fice daga jam’iyya APC zuwa jam’iyyar SDP
A wani bayani da Elrufai ya fitar ya ce sai da ya tuntubi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kafin ya sauya sheƙa.

Sai dai daga bisani shugaba Buhari ya jaddada matsayarsa wanda ya ce ya na nan daram cikin jam’iyyar APC babu gudu babu ja da baya.

A ziyarar da su ka kai a yau, Atiku ya ce sun kai ziyarar barka da sallah ne ga tsohon shugaban a gidansa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: