Shugaban hukumar kula da tuƙi a jihar Kano Baffa Babba Ɗan Agundi ya bayyana cewar akwai babur mai ƙafa uku da yawansu ya haura dubu 500, kuma za su taƙaitasu zuwa dubu 200.

“Adaidaita sahun da ake tuƙawa a jihar Kanoya yi yawa kuma sai mun taƙaitashi” cewar Baffa.

Baffa Babba ya bayyana hakan a gaban majalisar dokokin jihar kano inda ya ce waɗanda aka tantance za su sake rigista a hukumar.

Ga sauran matasa kuwa waɗanda suke tuƙa adaidaitan kuma ba su samu damar shiga tsarin ba, za su yi ƙoƙarin ganin gwamnatin kano ta samar da hanyoyin da za su samu abin yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: