Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC ta lalata gurɓatattun kayan abinci da darajar kudinsu ta kai naira biliyan 15.

Shugabar hukumar a Najeriya Mojisola Adeyeye ce ta sanar da haka a Ibadan babban birnin jihar Oyo.
An lalata kayan ne a jihar Oyo ranar Alhamis bayan gano waɗanda wa’adin su ya cika, da waɗanda ba su da inganci kuma ciki har da magunguna.

Shugabar ta ce za su ci gaba da tabbatar da tsare ingancin abinci da magunguna a Najeriya.

Ta ce lalata kayan da su ka yi zai taimaka wajen rage hatsarin amfani da grubatattun magunguna da kayan abinci a Najeriya.
Shugabar ta bukaci haɗin kan jami’an yan sanda, sojoji, DSS da sauran hukumomi don ganin an daƙile ɓarakar.
Sannan ta bukaci masu ruwa da tsaki da su wayar da kan jama’a a kan hatsarin amfani da magunguna da abinci marasa inganci.