
Hukumar Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) ta amince da sake buɗe rukunin tantance ɗalibai karo na ƙarshe har na tsawon awanni 48, domin jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi ba su kammala tantance dalibai masu nema ba. Wannan zai fara ne daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi, 12 Oktoba, har zuwa ƙarfe 12:00 na daren ranar Talata, 14 Oktoba. 
Daraktar Harkokin Sadarwa ta NELFUND, Mrs. Oseyemi Oluwatuyi ta ce an yi wannan ƙarin lokaci ne don tabbatar da cewa duk ɗalibai da suka cancanta sun shiga jerin wadanda za a tantance don samun Lamunin.


Tun daga ƙaddamar da shirin a ranar 24 ga Mayu, 2024, NELFUND ta karbi rejistar ɗalibai sama da 835,000 waɗanda suka nemi lamunin ta shafin hukumar na Intanet. 
Daga cikin waɗanda suka yi rejista, kimanin dalibai 510,378 ne suka sami lamunin. Adadin kuɗin da aka raba ya kai kimanin Naira Biliyan 9.5, inda ake biyan kuɗin makaranta (institutional fees) kai tsaye ga jami’o’i da kuma kudin kashewa (upkeep allowance) ga ɗalibai. 
Manufar NELFUND ita ce samar da lamunin ilimi mara ruwa (interest-free), domin ɗalibai su samu damar karatu ba tare da tsaikon rashin kuɗi ba. A farkon matakin aiwatar da shirin, an ƙayyade cewa kimanin ɗalibai miliyan 1.2 ne za su amfana da shirin zuwa shekarar 2025 daga jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandire na gwamnati da ke fadin kasar. 
Oluwatuyi ta yi gargadi ga jami’o’i da cibiyoyin da ba su kammala tantance ɗalibansu ba cewa idan ba su yi hakan ba cikin wannan ƙarin awanni 48, za su rasa damar shiga wannan zagayen lamunin. Ta kuma ce za a fitar da jerin sunayen jami’o’in da suka gaza tantancewa don a bayyana su a fili saboda dalibai su san inda matsalar take.