Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce gwamnatin kasar ta kafa kwamitin sasantawa da Amurka kan Matakin da ta dauka na dakatar da bayar da izinin shiga kasarta ga ‘yan Najeriya.

Fadar Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar.

Kwamitin wanda zai yi aiki karkashin ministan harkokin cikin gida, zai yi nazari tare da bitar ka’idojin da Amurka ta gindaya wa kasashen waje don ganin sun cika Ka’dojin AMURKA.

Gwamnatin ta ce a shirye take ta yi aiki tare da gwamnatin Amurka da sauran kasashe musamman ta fuskar tsaro.

Idan ba’a manta ba A ranar Juma’a 31 ga watan Janairu ne Amurka ta fitar da jerin kasashe shida da ta dakatar da bai wa takardun biza ciki harda Najeriya wanda Kuma duk kasashen musulmai ne ke da rinjaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: