Alhaji Muhammad Aminu Adamu da ake kira Abba Boss ya bayyana cewar talllafin da gwamnan Kano zai bawa alarammomi a kan batun almajiranci koma baya ne ga al’ummma.

Abba Boss ya bayyanawa mujallar Matashiya cewar, dalilin yin shelan hakan ya sa ana ta turo almajirai cikin gari ba tare da sanin adadinsu ba.
Cikin wata ganawa da Mujallar Matashiya ta yi da shi, ya ce babu wani dalili da zai sa iyaye suke turo yaransu Kano da sunan neman ilimin Addini, wannan fitina zai haifar saboda rashin nunawa yaran ƙauna da iyayen ba su yi ba tun a farko.

Ya bada shawarar cewar gwamnati ta tilastawa iyaye riƙe ƴaƴansu a gidajensu tare da amfani da makarantun boko, maimakon kawosu da ake da sunan almajiranci.

“Ana ta kawo yara almajirai waɗanda ba karatun suke ba sai dai su yi ta bara, don haka babu dalilin wannan furuci ya kamata gwamnati ta sake tsari.
“Gashi nan almajirai har sun cika gari duk inda ka yi ka gansu suna ta yawo suna bara wanda hakan barazana ne ga tsaro” Abba Boss.
