Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da tan Dubu saba’in daga ma’adanar hatsi ta kasa don raba wa mabukata a kasar nan a matsayin hanyar saukaka barnar da cutar coronavirus ta yi.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa a kan yaki da cutar COVID-19, Boss Mustapha, ne ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi karo na uku na PTF a ranar Laraba.
Kamar yadda yace, tan Dubu sittin sau dubu na hatsi za a raba wa jama’ar jihohi birnin tarayya Abuja, Legas da jihar Ogun.
Sauran tan goma sau dubu din kuwa za a raba ne ga mabukatan da ke sauran jihohin Najeriya.

Boss Mustapha Ya kara da cewa PTF ta habbaka dokoki da sabbin tsare-tsare yayin rufe jihohin nan, wadanda za su zagaye kasar nan ta hannun cibiyoyin tsaro.

Idan zamu tuna, a ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe jihohin Lagos da Ogun tare da babban birnin tarayya.
Hakan ta faru ne kuwa don hana yaduwar cutar coronavirus a kasar Najeriya.