Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar wahala sosai sakamakon annobar Coronavirus da kisan ‘yan bindiga.

Ya fadi hakan ne a jawabinsa na ranar yancin kai a ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni.

Ya ce: “Rana ce ta karrama magabatanmu wadanda suka yi wahala wajen samar da jumhuriyyarmu da duk wani dan Najeriya da ya yi aiki ba ji ba gani domin dorewar ta.

“Muna bikin damokradiyyar wannan shekarar duk da annobar coronavirus wacce ta raunana kasarmu da duniya baki daya.

“Shakka babu wannan lokaci ya kasance mawuyaci ga kowa, musamman wadanda suka rasa masoya sakamakon cutar. Da kuma wadanda suka rasa hanyoyin rike kansu sakamakon tsatsauran matakin da muka shimfida a kowani mataki na gwamnati domin magance annobar da tsare rayuka.

“Sadaukarwar ma’aikatan lafiyarmu da sauran masu muhimmin ayyuka wajen shawo kan wannan cutar ya nuna karfin gwiwarmu a matsayin mutane da kasa mai inganci.

Shugaban ya jajantawa al’ummar jahohin Katsina da kuma Borno kan kisan kiyashin da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa al’ummar Jahar.

Shugaba Buhari yace ” Ina cike da nadama da kuma takaicin abunda ya faru a jahohin Katsina, dakuma Borno kan Kisan al’umma da wasu tsageru sukayi”

“Jami’an tsaron kasarmu zasu zurfafa bincike tare da damka dukkan wanda aka samu da hannu a wurin aika-aika gaban kotu don fuskantar hukunci”

“Haka akwai bukatar al’umma su taimaka jami’an tsaro don samun damar magance wannan lamari”

“Ina kara jajantawa al’ummar jihohin Katsina da kuma Borno”.

Sai dai wasu na ganin akwai damuwa sosai kan yadda lamarin kashe-kashen jama’a ke ta kara yawaita a wadannan jihohi da kuma wasu sassa na Nijeriya.

“Kuma na yi amfani da wannan damar wajen mika godiya na ga dukkaninku a kan ayyukanku ga kasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: