Kwamishinan al’adun gargajiya da yada labarai na jihar Nassarawa, Dogo Shammah ya bayyana cewa gwamnati ta umurci duk kwamishinonin jihar da su killace kansu na tsawon kwanakin 14 domin guje wa kamuwa da cutar Covid-19.

Shammah ya ce haka ya biyo bayan kamuwa da cutar da kwamishinan Shari’a kuma Atoni-Janar din jihar Abdulkareem Kana ya yi.
Ya ce kwamishinonin sun killace Kan su daga ranar Juma’a bayan an dauki jininsu sannan su fito bayan sakamakon gwajin ya fito.
Gwamnan jihar Abdullahi Sule ya Sanar da haka a zaman da kwamitin zartarwar jihar a ranar 3 ga watan Yuli.

Kazalika Shammah ya yi Kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharruddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare kansu.

Zuwa yanzu dai mutane 236 ne Suka kamu da cutar a jihar Nasarawa.
Daga ciki 115 na kwance a asibiti, an sallami 113 sannan 8 sun mutu.