A yayin da ake fama da tsadar kayan masarufi a Najeriya, shinkafa ƴar Hausa ta kai naira 1,350 a Najeriya.

Farashin kayan abinci yayi tashin gwauron zabi ne a yayin da ake ƙara shiga yanayin damuna a wasu ƙasashen duniya.
A jihar Kano, Mujallar Matashiya ta zanta da wani ɗan kasuwa da ya buƙaci a sakaye sunansa wanda ya bayyana cewar a kullum kayan masarufin na ƙara samun saabon farashi a kasuwa.

Ya bayyana cewar a shinkafar da ake nomawa a Najeriya ana siyar da ita naira 1350, sannan akwai ta ƙasa da haka amma farashin ya fara ne tun daga naira 1200.

Farashin gero kuwa ya kai naira 550 a duk mudu yayin da ake siyar da masara naira 500.
Ɗan kasuwar ya bayyana cewar a wata kasuwar jihar Kano hatta fulawa idan mutim zai siya sai an bashi ƙa ida na siyan wani abin ko da kuwa bai yi niyya ba, baya ga tsadar da fulawan ta ƙara wadda a yanzu ake siyar da mudunta naira 700.
Wasu da muka zanta da su sun bayyana cewar, a kullum idan suka je siyan katan masarufi suna samun sabon farashi saɓanin yadda suka siya a baya.
Idan ba a manta ba a jihar Kano an yi tsari na daidaita farashin kayan masarufi a lokacin da ake gudanar da azumin ramadan, sai dai wancen tsari, tuni ƴan kasuwa suka yi fatali da shi wanda a yanzu kowa yake saka farashin da yayi daidai da ra ayinsa.
Za mu ji ta bakin shugaban hukumar karɓar ƙorafe ƙorafe a jihar Kano don jin inda wancen tsari ya tafi a yanzu.