Sarkin Sharifan Kano Ya Yabawa Gwamna Ganduje Wajen Kare Martabar Annabi Muhammad (SAW) Da Addinin Allah

Kwanan baya ne Sarkin Sharifan Kano Sidi Fari ya yabawa hobbasar da Gwamnan jihar ta Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ke yi wajen kare martabar Annabin Tsira Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma kokarin da ya ke wajen ganin Addinin Musulunci ya kara habaka.
A yayin da Gwamnan yake karbar tawagar Sharifan daga Zawiyyoyi da majalisun Sharifan daga fadin jihar ta Kano a babban dakin taro na Africa House, da ke Gidan Gwamnatin Kano, ya kara tabbatar musu da cewa ire-iren addu’o’in da su ke yi ne tare da malamai da ke jihar da daukacin al’umma, shine jihar ta ke cikin zaman lafiya.

Gwamnan ya yi dan tsokaci kadan wajen irin gudummmawar da Sharif Sheikh Abdulkareem Al-Maghili ya bayar wajen tabbatuwar adalci a mulkin jama’a da kuma bayar da tsari na musamman wajen yadda sha’anin mulki ya kamata ya zamo, tun daga lokacin da ya shigo wannan jiha ta Kano.

Ya ce “Wannan dalilin ne ya sa mu ka sa wa Hukumar Shari’ah ta jiha da sunan Sheikh Al-Maghili. Domin tunawa da irin gudummawar da ya bayar a wannan jiha ta mu ta Kano. Sannan wani abin alfahari kuma shine, kasancewarsa shi ma Sharifi jinin Ma’aikin Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.”
Ya kuma tabbatarwa da Sarkin Sharifan cewa gwamnatin Kano za ta karasa ginin Zawiyyar Fadhima dake Kantudu a unguwar Sharifai. Baya ga kira da Sarkin Sharifan ya yi fa gwamnati da ta shigo wajen ganin kammaluwar ginin.
“Mu na kuma kara godiya wajen yi mana addu’o’i na musamman da a ka yi lokacin da mu ke tsananin fuskantar annobar COVID-19. Alhamdulillah mu na da labarin irin addu’o’i da a ka dukufa a ka yi mana gaba daya. Wannan ya kara nuna yadda ku ke da kishin wannan jiha ta mu da ma kasa baki daya,” in ji Gwamnan.
Da ya yi magana a madadin Sarkin Sharifan, Shugaban Majalisar Dattawa ta Shurafa’u a Kano, Sharu Tijjani Ibrahim, ya tabbatarwa Gwamnan na Kano, jin dadin da Sharifan Kano suke ji saboda kulawa ta musamman da gwamnatin Ganduje ke ba su. “Tare da share mana kukanmu duk lokacin da mu ka kawo kukanmu ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano,” ya ce.
“Maigirma Gwamna mu na kara nuna maka goyon bayanmu wajen kokarin da kake don ci gaban wannan babbar jiha ta mu ta Kano. Kullum ba ma gajiyawa wajen yi maka addu’o’I saboda neman tallafi daga Allah, Ya sa ka gama lafiya,” in ji shi.
Daga karshe Sarkin Sharifan ya yi wata addu’a ta musamman ga Gwamna Ganduje. Shi kuma Gwamnan ya kara yabawa da Sharifan saboda wannan babbar ziyara da su ka kawo masa har fadar gwamnati.
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labarai
Na Gwamnan Jihar Kano
Laraba, 2 ga Watan Satumba, 2020
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com