Babbar kotun jiha da ke zamanta a Ringim jihar Jigawa ta yanke wa wasu matasa biyu Mustapha Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Da yake karanta hukuncin Alkalin kotun mai shari’a Ahmed Muhammad Kazaure ya ce kotun ta samu Mustapha Idris da laifin kashe wata budurwa ta hanyar ska mata wuƙa a maƙogaronta.
Al’amarin ya faru tun a ranar 12 ga watan Janairun da muke ciki kuma kotun ta gamsu da kwararan shaidun daaka gabatar mata wanda ta samu Mutapha da kashe Nafisa Hashimu.

An yake wa Mustapha hukuncin ne ƙarƙashin sashe na 221 (a) na kundin dokokin jihar Jigawa.
