Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace matafiya 18 a jihar Ondo.

Ƴan bindigan sun sace mutanen ne a kan hanyar su ta zuwa Legas.

Al’amarin ya faru ne ranar Laraba a Idoani-Ifira da ke ƙaramar hukumar Akoko ta Kudu  a jihar.

Ƴan bindigan sun fara harbin iska ne a yayin da su ka tare babbar hanyar lamarin da ya sa mutane su ka fara tsere wa don tsira da rayuwar su.

Ƴan bindigan sun shige cikin daji da mutanen da su ka sace.

Baturen ƴan sanda a yankin ya tabbatar da cewar sun samu labarin abin da ke faruwa kuma sun a aiki tare da sauran jami’an tsaro don kuɓutar da su.

Wata majiya daga ɓangaren iyalan wasu da a ka sace sun bayyana cewar maharan sun buƙaci a basu naira miliyan hamsin kafin sakin mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: