Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2023 a matsayin rannar da za a yi zaben shugaban ƙasa.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka ya na mai cewa lokaci na ƙara ƙurewa a kan sabuwar dokar zabe da aka sabunta a shekarar 2021.

Hukumar ta buƙaci samar da dokar da za ta yi aiki a zaɓe mai zuwa kafin watanni 12 zuwa 18 gabanin gudanar da zaɓe.

INEC ta sanar da cewar ta na yin dukkanin ayyukanta ne bisa doron dokar da aka tsara wa hukumar, hakan ya sa ta ke son ganin an kammala aikin samar da sabuwar dokar wadda za ta bayar da damar aiki da ita a zaɓen shekarar 2023.

Gyaran dokar hukumar zaɓe dai ya haifar da zazzaafar muhawara musamman zaɓen ƴar tinƙe ga dukkan jam’iyyu da kuma sanar da sakamakon zɓe a kafar Intanet.

Tuni majalisa ta miƙa wa shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari sabuwar dokar hukumar zaben wanda ya cika wa’adin da doka ta ba shi dama na wata guda domin sanya hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: