Tsohuwar Jami’iyyar da tai mulki a Najeriya PDP ta gargadi gwamnan Jihar Kano da kada ya karbi kudade a hannun masu makarantu masu zaman kansu.

Gargadin hakan ya fito ne ta bakin shugaban Jam’iyyar reshen Jihar Kano Shehu Sagagi shi ne ya bayyana a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Yace kada gwamna Ganduje ya yi amfani da wannan dama wajen sanya wa makarantu masu zaman kasan kudade yayin sake tantance su.

Jam’iyyar ta ce dama akwai wasu ka’idoji da kasa ta ke sanya wa makarantu masu zaman kansu tun kafin su bude wanda gwamnatin baya ta samar da shi.

Jam’iyyar ta yi kira ga gwamnan da ya bi doka da ka’idoji domin sanya ido a kan makarantu masu zaman kansu wajen ganin an gudanar da gyara yanda ya kamata.

Jam’iyyar ta kuma yaba wa hukumomin tsaron Najeriya kan yadda su ke jajircewa akan shari’ar Hanifa Abubakar dalibar da ake zargi malamin su ya hallaka ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: