Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya bukaci al’ummar Najeriya musamman mazauna birnin tarayya Abuja da su kwantar da hankalin su a kan ƙarancin man da ake fuskanta.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar bayan samun dogayen layi a gidajen mai a wasu sassan Abuja, kamfanin ya ce akwai isashshen mai da zai wadata yan ƙasar.
Kamfanin ya bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗa wa a kan karancin man fetur da za a iya fuskanta ba da jima wa ba.

An samu karancin man fetur a gidajen mai a Abuja bayan da gwamnatin tarayya ta yi watsi da aniyar janye tallafin mai a makon da mu ke ciki.

Wasu gidajen mai a Abuja sun kasance a rufe yayin da masu siyar da mai a jarka wadanda aka fi sani da bumburutu su ke cin kasuwarsu.
Jita-jitar samun ƙaracin mai ya sa mutane da dama su ka haɗa cunkoso domin siyan man da zai ɗauke su tsawon lokaci su na buƙata da shi.