Daga Amina Tahir Muhammad

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da kama wasu masu garkuwa da mutane, wadanda ake kyautata zaton suna da hannu wajen kashe jami’an ‘yan sanda biyu, da yin garkuwa da surukin wani dan kasuwa da sauran miyagun ayyuka a yankin Arewa maso yammacin jihar.

Hakan dai ya biyo bayan farmakin da aka kai wasu maboyar ‘yan ta’adda guda uku a kauyukan Dajin Maizuwo, Dan Gwanki da Yandamo dake karamar hukumar Sule Tankarkar ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Sale Tafida, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar da ke Dutse a ranar Alhamis, ya ce an cimma nasarar hakan ne biyo bayan samun rahoton sirri da aka samu.

An yi holen mutane 14 da suka hada da maza goma da mata hudu, ciki har da wanda ake zargin ƴan asalin jihar Kaduna ne.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da AK-47 guda uku, harsashi 308 mai girman mita 7.6, Bindigogin Mashin Janar guda daya, (GPMC), tsabar kudi naira miliyan biyu, Addina, wayar  salula shida da sauran kayayyaki.

Idan ba a manta ba Mujallar Matashiya ta kawo muku labarai a kan sace wani mutum a jihar tare da hallaka ƴan sanda biyu a ƙarsehn makon da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: