Rundunar yan sanda a jihar Neja sun kuubutar da wasu mutane 20 waɗanda yman bindiga su ka yi garkuwa da su..

Mai magana da yawun rundunar DSP Wasiu Abiodun ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi.

Ya ce an kuɓutar da mutane 20 bayan fafatwa da su ka yi da yan bindigan ta hanyar musayar wuta.

Kakakin ya ce sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ƴan bindigan a yayin musayar wutar da su ka sannan sun kuɓutar da wasu shanu waɗanda ƴan bindiga su ka sace.

Ya ƙara da cewa nasarar kubutar da mutanen sun yi aikin ne hadin guwiwa da sauran jami’an tsaro kamar soji da ƴan banga.

Sannan jami’an sun yi nasarar ƙato wasu makamai daga hannun ƴan bindigan daga ciki akwai biondigu ƙrar AK47, sai harsashi mai yawa da kuma babur guda ɗaya.

Abiodun ya ce an shafe kimanin awanni biyu ana fafatawa da ƴan bindigan yayin da su ke koƙarin guduwa bayan tara-tarar da jami’an tsaro su ka yi musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: