Ƙasar Pakistan sun bayyana cewa sun samu Rahoton cewa ƙasar Indiya na shirin kawo mata hari.
Ministan harkokin wajen ƙasar pakistan Shah Mahmood Qureshi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Inda yace sun samu ƙwaƙƙwaran rahoton cewa ƙasar indiya na shirin kawo mata hari a wannan wata na Afrilu da muke ciki.
A cewar Mahmood tuni suka sanar da kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya kan wannan yunƙuri na ƙasar Indiya.
Idan ba’a manta ba ƙasashen biyu sun daɗe suna taƙun saƙa da juna, sai dai abaya bayannan rikicin ya ƙara tsami tun bayan da wani ɗan ƙunar bakin wake ya tada bom a yankin Kashmir dake indiya wanda yayi sanadin mutuwar ƴansanda 40.
A ɓangare guda kuma kakakin Indiya Ravesh kumar ya musanta wannan zargin na ƙasar Pakistan tare da watsi da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: