Gwamnatin ƙasar New Zealand ta tura jami’an tsaro na musanman domin kwato wata jami’ar lafiya ta ƙasar mai suna Louisa Akavi,mai shekaru 62 wacce mayaƙan IS suka yi garkuwa da ita a ƙasar Syria tun a shekarar 2013.
Hakan ya biyo bayan da ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa wato Red Cross da ta ke yi wa aiki ta ce ta samu wasu bayanai da ke tabbatar ma ta da cewa jami’ar yar na nan da ranta.
An dai sace ma’aikaciyar lafiya tare da wasu direbobi biyu ƴan Siriyan a lokacin da ta ke tsaka da aiki ne a shekarar 2013, sai dai tun wancan lokacin ba a samu isassun bayanai da za su taimaka wajen gano inda aka ajiye mutanen ba.
Ana ta ɓangaren Red Cross ta ce, manema labarai sun guji yaɗa labarin garkuwa da ma’aikatan domin gudun jefa rayuwarsu cikin haɗari.
Sai dai A yau ne gwamnatin New Zealand ta sanar da tura runduna ta musamman don kwato matar da kuma direbobin da aka ce wanda har yanzu suke hannun ƙungiyar IS.

Leave a Reply

%d bloggers like this: