Mata adon gari
Yadda za ki kare kanki daga cutar sanyi – Adon Gari
Daga Mariya Murtala
Ga wadanda suke biye da mu ta cikin wannan shafi mai albarka, a watan da ya gabata mun kwana a dai dai lokacin da za mu kawo hanyoyin da ake kaucewa kamuwa da cutar sanyi, amma a wannan karon za mu duba illar da hakan kan haifarwa mata musamman masu aure.
Sanin kowa ne dai duk macen da ta cika mace kuma ta san wacece ita, ta kan gyara jikinta musamman don gudun kamuwa da cutar sanyi amma akwai illar da hakan kan haifar wanda a lokuta da yawan gaske aure na rabuwa sakamakon rashin gamsuwa da mijin kan yi idan mace na ɗauke da cutar sanyi.
Wasu matan ma wani ɓangare na jikinsu na zubar da ruwa mai wari ko kuma kumburi na babu gaira babu dalili.
Wannan kan sa miji ya tsani matarsa, idan kuma aka yi rashin sa a shi ma yaɗauki cutar, babu mamaki matarsa ba ɗaya bace dukkansu ya shafa musu wannan cuta ta sanyi.
Na san da yawan mata na sane da duk abinda na faɗa don ba komai na faɗa ba cikin illolin da sanyi kan haifarwa mace a lokuta da dama.
Idan kin kasance kina ɗauke da wannan cuta, ko kuma kina daar uwa da ke ɗauke da wannan cuta, ki bata labarin mujallar Matashiya domin a nan ne za mu fara kawo hanyoyin da za a bi don rabuwa da cutar bakiɗaya.
Da farko idan kina ɗauke da cutar sanyi, wanda bai yi yawa a jikinki ba za ki fara gwada waɗannan hanyoyin kamar haka.
Na farko a kullum da safe za ki samu ruwan ɗumi amma ba mai zafi sosai ba kuma ki tabbata ruwan mai kyau ne sosai da sosai abin da za ki zuba ma ki tabbatar yana da tsafta sosai, bayan kin zuba ruwan zafin a cikin roba mai girma wadda za ki iya shiga ciki ki zauna, sai ki samu wajen mai kyau ko da banɗakin da za ki amfani da shi ma ki tabbatar yana da tsafta sosai kin san idan za a yi maganin cuta sai an kaucewa duk wata hanya da za a iya samun wata cutar.
Za ki samu ruwan nan ki shiga ciki, ki ɗauki kamar minti 30 a ciki ba tare da kin tita ba.
Kash, lokaci ya cimmana a yanzu amma mu tara a fitowa ta gaba don ɗorawa daga inda muka tsaya.
Mata adon gari
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari
Tare da Zainab Sani Usman
A cigaba da kawo muku kayatattun sinadaran kayan gyaran jiki a yau shafin naku na mata adon gari zai cigaba da kawo muku sinadarin da zakuyi amfani dashi don gyaran gashin mu.
Kamar yadda a lokacin sanyi muka dage wajen kula da gashinmu to haka ma a yanzu zamu dage wajen kula dashi domin kuwa idan muka ce zamu tsaya to lalle zamu zama abin kyamata dan duk wadanda suke makusantanmu zasu dinga jin irin tashin tsamin da gashin zai dinga yi, wasu zasu iya fadamaka wasu kuwa suna jin nauyin su ce kanka yana tsami ko wari.
Wannan tasa naga ya dace mu dage mu kula da kanmu kuma a lokacin nan na zafi ma kanka damunka zai yi gashin idan ba’ayi kitso ba.
HADI NA DAYA.
1, Man Zaitun
2, habbatussauda
3, kwanduwar kwai
A samu kwanduwar kwai banda ruwan, a hada da cokali daya na habbatussauda, cokali daya na man zaitun a hada su guri guda, bayan sun hada jikinsu sosai a shafa a kai sosai ko’ina yaji da yamma za’a shafa idan gari yaw aye sai a wanke da ruwa mai dumi, idan ya fita tas ya bushe a shafa mai dai dai misali ayi kitso akalla dai duk sai sati ya kamata a dinga yin kitson kuma duk yi a wanke kan kafin yin kitson.
HADI NA BIYU
1, Man zogale
2, man zaitun
3, man kwakwa
4, man alayyadi
Shi kuma wannan hadin kullum za’a dunga shafawa a gashi idan an fito da ga wanka, idan kitso ne akan mutum sai a dinga bin layin kitson ana shafawa idan kuma kan a tsefe yake sai a dinga tsaga gashin da kibiya ana shafawa har a gama.
HADI NA UKU
1, Ganyen Magarya
2, Man Zogale
3, kanun fari kadan
A daka ganyen magarya a hada da man zogale da kanun farin kadan a dinga shafa wa gashi shima wannan hadin yana gyara gashi sosai.
Haka kuma kamar yadda na fada a baya yawaita cin wadannan kayannan yana kara kaurin gashi da yawansa sannan kuma gashin yayi baki.
1, Cukwui
2, Man zaitun
3, Cucumber
4, Man shanu
Da fatan zamu cigaba da dagewa muna gwada dukkan abubuwan da muke kawowa.
Muna fatan zaku cigaba da bibiyar mu don kawo muku kayatattun sinadaran kayan gyaran jiki.
Allah ya sa da mu da Albarkar wannan wata da yake tunkaro mu na Ramadan amin summa amin.
Mata adon gari
Yadda za ki kaucewa cutar sanyi – Mata kawai
Daga Mariya Murtala
Ga wadanda suke biye da mu ta cikin wannan shafi mai albarka, a watan da ya gabata mun kwana a dai dai lokacin da za mu kawo hanyoyin da ake kaucewa kamuwa da cutar sanyi, amma a wannan karon za mu duba illar da hakan kan haifarwa mata musamman masu aure.
Sanin kowa ne dai duk macen da ta cika mace kuma ta san wacece ita, ta kan gyara jikinta musamman don gudun kamuwa da cutar sanyi amma akwai illar da hakan kan haifar wanda a lokuta da yawan gaske aure na rabuwa sakamakon rashin gamsuwa da mijin kan yi idan mace na ɗauke da cutar sanyi.
Wasu matan ma wani ɓangare na jikinsu na zubar da ruwa mai wari ko kuma kumburi na babu gaira babu dalili.
Wannan kan sa miji ya tsani matarsa, idan kuma aka yi rashin sa a shi ma yaɗauki cutar, babu mamaki matarsa ba ɗaya bace dukkansu ya shafa musu wannan cuta ta sanyi.
Na san da yawan mata na sane da duk abinda na faɗa don ba komai na faɗa ba cikin illolin da sanyi kan haifarwa mace a lokuta da dama.
Idan kin kasance kina ɗauke da wannan cuta, ko kuma kina daar uwa da ke ɗauke da wannan cuta, ki bata labarin mujallar Matashiya domin a nan ne za mu fara kawo hanyoyin da za a bi don rabuwa da cutar bakiɗaya.
Da farko idan kina ɗauke da cutar sanyi, wanda bai yi yawa a jikinki ba za ki fara gwada waɗannan hanyoyin kamar haka.
Na farko a kullum da safe za ki samu ruwan ɗumi amma ba mai zafi sosai ba kuma ki tabbata ruwan mai kyau ne sosai da sosai abin da za ki zuba ma ki tabbatar yana da tsafta sosai, bayan kin zuba ruwan zafin a cikin roba mai girma wadda za ki iya shiga ciki ki zauna, sai ki samu wajen mai kyau ko da banɗakin da za ki amfani da shi ma ki tabbatar yana da tsafta sosai kin san idan za a yi maganin cuta sai an kaucewa duk wata hanya da za a iya samun wata cutar.
Za ki samu ruwan nan ki shiga ciki, ki ɗauki kamar minti 30 a ciki ba tare da kin tita ba.
Kash, lokaci ya cimmana a yanzu amma mu tara a fitowa ta gaba don ɗorawa daga inda muka tsaya.
-
Labarai10 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari