Tare da Abdurrahman Ibrahim Zage

*SHIMFIDA*
Da sunan Allah ma’abocin rahama da jin k’ai.
Tsira da amincinsa su k’ara tabbata ga shugaban talikai (SAW) da ahalinsa da sahabbansa da wad’anda suka bi tafarkinsu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya kai d’an uwa musulmi! Cike da farin ciki da shauk’i nake taya ka murnar gabatowar watan Ramadan, wata mai alfarma da daraja, watan rahama da gafara, watan da Allah yake shelar baje-kolin falala da karamcinsa ga bayinsa, muminai da fajiransu, watan da ke farkar da bayin Allah daga magagin gafala, da narkar da su daga daskarewa cikin sab’a masa, ya sanya su bibiyar aiyukan da suka gabatar a shekarar da ta gabata, domin tuba da gyara kura-kuransu, tare da fuskantar Allah (SWA) da zuciya tsaftatacciya, ta hanyar yawaita tuba da aiyukan alkhairi.
Hakika d’an tak’i kad’an ya rage mana, mu karb’i bak’uncin watan Ramadan mai albarka, don haka ya kai D’an uwa! tambayi kanka; wanne shiri ka yi na tarb’ar wannan bak’o mai girma?
Hadisi ya tabbata daga Annabi (SAW) a k’arshen watan Sha’aban yana cewa;” Ya ku mutane! Lallai wani wata mai girma zai yi muku inuwa, watan albarka, watan da ya ke da wani dare, wanda aiki a cikinsa yake dai-dai da aiki a wasu wattani dubu(wanda ba shi ba)…..Shi ne watan da farkonsa rahama, tsakiyarsa gafara, k’arshensa kuma ‘yantuwa daga wuta”
A wata ruwayar daban. Annabi (SAW) ya ce: “Ya ku mutane! Hakika watan Allah mai albarka ya fuskanto ku da albarka da rahama da gafara, shi ne watan da ya fi sauran watanni falala a gurin Allah, yininnikansa sun fi sauran yininnika, kuma dararensa sun fi sauran darare, sa’arsa ta fi sauran sa’o’i falala. Shi ne watan da aka kiraye ku zuwa liyafar Allah, aka maida ku ahalin karamcin Allah a cikinsa, numfarfashinku a cikinsa tasbihi ne, barcin ku ibada, aikinku karb’abb’e ne, addu’arku amsasshiya ce”
Don haka yakamata ga duk mumini ya nace da rok’on Allah ya ba shi ikon ganin wannan wata mai girman falala, ya taimake shi a kan azumtarsa da tsayuwa a cikinsa yana mai imani da neman lada a gurin Allah.
Ka tuna yawan mutanan da ka azumci Ramadanan shekarar da ta shige tare da su, amma yau babu su, sun amsa kiran mahaliccinsu,, toh kamar haka ma wasu mutanan da suke raye yau, ajalinsu zai yanke da su, ba za su ga wannan wata mai girma ba, duk da k’arancin kwanakin da suka rage masa. Toh ka yawaita addu’a Allah yasa kana daga cikin wad’anda za su karb’i bak’uncin wannan bak’o mai girma.
Hakika farin ciki da rabauta sun tabbata ga bawan da ya sabunta tubansa ga Allah (SWA), kafin isowar wannan bak’o mai girma tun yanzu, domin ya rayu yana wankakke daga zunubansa a cikin Ramadan, sakamakon tuba na gaskiya, da tsarkin niyyar bawa ta nisantar dukkan abinda Allah ya haramta…
Allah ya ‘yantar da mu daga azabarsa, yasa mu ga Ramadan cikin rai da isasshiyar lafiya!!!

Leave a Reply

%d bloggers like this: