Daga Sadisu Dada

Ƙungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid ta Samu Nasarar Daukar dan wasa Luca Jovic wanda manyan kungiyoyi ke zawatcinsa wanda suka hada da Barcelona, Bayern Munich da ita kanta Real Madrid.
Dan wasa Luca Jovic dan Asalin kasar Serbia ya kasance Mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Frankfuit da take kasar Jamus, Luca Jovic zai koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ne kan kudi €60 wanda tsohuwar kungiyarsa ta Benfica zata rabauta da kudi €12 inda sauran kudin zasu shiga Lalitar Kungiyarsa.
Luca Jovic ya buga wasanni 44 a wannan kakar wasa yayinda ya zura kwallaye 26

Leave a Reply

%d bloggers like this: