Connect with us

Al'ada

Akwai garin Rano tun shekaru 300 kafin zuwan Annabi Isah

Published

on

Mai martaba sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila Autan Bawo ya bayyana cewar akwai ƙasar Rano wadda ke cikin Hausa bakwai tun shekaru 300 kafin zuwan Annabi Isa.

Sarkin Rano ya bayyanawa mujallar Matashiya cewar dawo da darajar masarautar abin alfahari ne tare da ɗaukar azamar cigaba da ayyuka tuƙuru na yadda al’umma za su amfana.

 

Cikin zantawa da ya yi da mujallar Matashiya ya ce ƙasar Rano na da daɗaɗɗen tarihi wanda duniya ma ba za ta manta da shi ba ganin manyan al’adu da ke kewaye da garin.

Batun nasarorin da ya samar a matsayinsa na sarki kuwa, mai martaba sarkin rano ya bayyana ɗumbin nasarorin da ya samawa al’ummarsa tun bayan hayewa kan karagar mulki, nasarorin da suka haɗa da inganta ilimi, harkokin kasuwanci da kuma ɓangaren lafiya.

 

Haka kuma ya bayyana cewar masarautar Rano dama tun fil’azal tana da daraja ta ɗaya a halin yanzu dawo da wannan darajar aka yi don haka ba sabon abu bane kamar yadda wasu mutanen ke kuskuren fahimta.

Sannan ya ja hankalin hakiman da ke ƙarƙashinsa da su kasance masu ƙoƙarin kawo hanyoyin da al’ummar masarautar za su cigaba kamar yadda ya yaba da ƙoƙarin da suke yi a baya.

Za ku iya kallon hirar a dandalin mujallar Matashiya da ke youtube.

Click to comment

Leave a Reply

Al'ada

Aminu Ado ya zama shugaban majalisar sarakunan Kano na dindindin

Published

on

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne zai ci gaba da shugabantar majalisar Sarakunan Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yasanya hannu kan dokar da ta haramta tsarin karɓa-karɓa na shugabancin majalisar sarakuna a Kano.

Sabuwar dokar ta bawa mutane biyar damar naɗa sarki a kowacce masarauta saɓanin mutane huɗu da ke naɗa sarki a baya

Gidan shatima shi ne sakatariyar masarautar wanda a yanzu haka ake gyarawa.

Gwamnan Kano ganduje dai ya ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu aka basu sanda a zamanin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll.

Continue Reading

Al'ada

Shekara biyar da rasuwar marigayi Ado Bayero

Published

on

Ya rasu a ranar 6/6/2014 bayan doguwar jinya da ya yi.

Allah ya gafartawa mai martaba sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero.

Continue Reading

Al'ada

Maimakon hawan Ɗorayi, za a yiwa marigayi Ado Bayero Addu a a fadr Kano

Published

on

Ramadhan: Hudubar Jumu'a Malam Muhammadu Sanusi II 17-05-2019

Masarautar kano ta bada sanarwar cewa ta dakatar da hawan ɗorayi inda ta maye gurbinsa da yiwa marigayi Ado bayero addu ar shekaru biyar da barinsa duniya.

Sanarwar wadda aka aike da ita ta ƙunshi amincewa da bin umarnin gwamnati na dakatar da hawan Nassarawa.

Wannan dai babban al amari ne ganin cewar ba a taɓa makamancin haka ba a kwanaki mafi kusa.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: