Alhaji Maifada Ali Yakubu yayi bikin cikar shekararsa 30 kan karagar mai unguwar Gama b.
taron yasamu dubban al’umma da suka halarta domin tashi murna, kafin washe garin ranar angudanar da wasanni na gargajiya kala.
mujallar matashiya ta samu damar ganawa dashi a gurin yayin da ya bayyana mana da cewar yana cike da farin cikin da bazai musaltuba, sannan yana yiwa kowa fatan alkairi.
anasa bangaran Dagacin Gama ya halarci gurin shima domin taya mai unguwar wannan murna, shima yayi jawabi da cewar mai unguwar ubane abin koyi ga al’umarsa domin ya tsaya kai da fata wajen duk wani abu mai muni ko mara kyau baya goyon bayansa ko kadan, sannan mutum ne mai jin kukan mutanensa, akarshe yayi fatan alkairi ga al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: