A yau lahadi ne aka gabatar da taron kaddamar da kungiyar cigaban garin Gasau dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Shugaban kungiyar Abubakar Mu’awuya Gasau ya bayyanawa Mujallar Matashiya cewa sun kafa wannan kungiyar ne domin yada ilimi da kuma bunkasa cigaban garin, kungiyar dai zata maida hankali wajen samar da Ilimi ga matasa, samar da aikin yi da tallafawa marayu da marasa gata.

Taron wanda ya gudana a garin na Gasau ya samu halartar Dagacin garin Alhaji Usman Tukur, Farfesa Muhammad Bello Shitu daga jami’ar Bayero, dan gwagwarmaya Zafrullahi Abdullahi, da kuma Kwamaret A.A Haruna Ayagi, dalibai, da sauran al’umma da dama.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: