Tsohon shugaban makarantar sakandire ta Suntulma Gama Sani yakubu ne ya bayyana hakan yayin taron tsofaffin ɗalibanmakarantar aji na 2010.

Ya ce jajircewar ɗaliban ne ya sa ƙungiyar ɗaliban ke cigaba wanda har ta kai a halin yanzu suna bada gudunmawa ga al umma baya ga su kansu.

Wannan ƙungiya dai an samar da ita ne bisa jagorancin shugabannin ƙungiyar Murtala Idris Hamza Abdullahi da Sulaiman Gama.

Shugaban ƙungiyar ya ja hankalin sauran ɗalibai da su kasance masu jajircewa don hakan na tabbatar da nasara ga mutanen da akai zaman makaranta ɗaya.

Taron wanda aka yishi a makarantar Suntulma da ke Gama, kuma ana gudanar da shi duk shekara.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: