Gwamnan kano Abdullahi umar Ganduje ganduje ya umarci hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kano, da ta gudanar da bincike kan wani rahoton da ake cewa wani gaggon biri ya haɗiye naira miliyan shida da dubu ɗari takwas, a gidan ajiye namun daji (ZOO) dake jihar kano.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnatin kano Abba Anwar ya fitar, ya bayyana cewa gwamna ganduje ya umarci hukumar da ta gaggauta wannan binciken akan al’amarin.

Kuɗin dai sunyi ɓatan dabo ne a gidan ajiyan namun dajin inda ake tsaka da gudanar da bukukuwan ƙaramar sallah, kuma aka alaƙanta goggon birin da lashe maƙudan kuɗaɗen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: