Yan tada kayar baya da masu garkuwa da mutane a jihar zamfara sun bayyana sharudansu ga gwamnati indai ana so su ajiye makamansu.

Kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar Usman Nagogo ya bayyana matsayar yan bindigar ne a lokacin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro na jihar zamfara.

Cikin sharudan da yan ta’addar suka gindaya, sunce dole ne a daina kashe fulanin da ake zargi a kasuwanni kauye da wasu jami’an sa kai ke yi a jahar.

Haka zalika sun kuma bukaci a basu damar zuwa kasuwanni ba tare da sun fuskanci tsangwama ba a wurin jami’an tsaro.

A cewar kwamishinan yan sandan wannan sharudan nasu da suka rubuto ya biyo bayan yunkurin da gwamnati take don ganin anyi sulhu da su ka na su ajjiye makamansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: