Shugaban Kwalejin ya shaidawa manema labarai cewa sun ƙone wayoyin hannu na miliyoyin nairori da suka kwace daga hannun ɗalibai wanda suke satar jarrabawa.

Haka kuma aka ƙone wayoyin a filin makarantar.
Mataimakin shugaban makarantar Bayo Oyeleke ya ce satar jarrabawa babban laifi ne a makarantar kuma sun yi hakan ne da nufin tsaftace ilimin ɗaliban jihar.

