Wasu mutane da suka rufe fuskokinsu sun Kai farmaki a tashoshin jiragen kasa dake lardin Hong Kong a ranar lahadi.
An hango mutanen ne da na’urar daukan hoto ta dauka sanye da fararen kaya suna far wa mutanen da kuma kwace musu kayayyakinsu.

Rahotanni dai sun tabbatar da Akalla mutane 40 ne suka jikkata sai dai babu rahoton rasa rai, sai Mutum daya da yake cikin mawuyacin hali.

Al’amarin ya biyo bayan lokacinda jami’an tsaro suka harba barkonon tsohuwa tare da harba harsashin Roba akan wasu masu zanga zanga kan suna son su tabbaatar da tsarin dimokaradiya a Yankin, yanzu haka dai jami’an yan sanda sun dau Alwashin kawo karshen lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: