Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun gudanar da Zanga-Zangar lumana a jihar Adamawa, don nuna fushinsu dangane da yadda ake samun yawaitar fyade a fadin jihar.

Da yake jawabi a gaban masu zanga-zangar Gwamnan jihar Adamawa Ahmad Umaru Fintiri ya ce aikata fyade a jihar zai zamo tarihi kasancewar gwamnati tayi shiri na musamman don dakile wannan mummunar Ta’ada a fadin jihar.
Haka zalika gwamnan ya shawarci iyaye dasu Kasance masu sanya ido akan yaransu, ko da yaushe da kuma kula da yanayin mu’amalarsu haka ne zai taimaka wajen ganin an magance matsalar.

