Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa jami an tsaro bisa kuɓutar da yara tara da aka sace aka siyar da su a jihar Anambara.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar a yau, Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ƙara ƙaimi don ganin an samu cikakken tsaro a jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya jinjinawa jami an ƴan sandan da suka yi wannan hoɓɓasa tare da sauran jami ai da ke aiki ba dare ba rana don ganin an samu wadataccen tsaro a jihar Kano.

Sannan ya ja hankalin iyaye da su ƙara sa ido a kan ƴaƴansu don ta hakan ne za a magance faruwar hakan a nan gaba.

Idan ba a manta ba rundunar ƴan sandan jihar Kano ce ta ceto wasu yara ƙanana guda tara da aka yi cinikinsu a jihar Anambara inda ake bautar da su har ma aka sauya musu addini.

Leave a Reply

%d bloggers like this: