Yayin ƙaddamar da shirin binciken kwakwaf kan satar yara a Kano wanda ya samu halartar ƴan kwamitin, gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bada umarnin yin hukuncin kisa ga mutanen da aka samu da laifin aikata garkuwa da mutane.

Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar a yau, gwamna Ganduje ya ce tuni ya bada umarni ga ma aikatar shari a don sauya dokar garkuwada mutane daga rayuwar gidan ɗan kande zuwa hukunvin kisa.
Yayin zaman ƙaddamar da kwamitin bincike kan satar yara a Kano, kwamitin zai binciki matsalar ɓatan yara tun daga shekarar 2010.

Haka kuma shugaban kiristocin Najeriya reshrn jihar kano ya bada goyon bayan hukunta waɗanda aka samu da aikata laifin satar ƙananan yara tare da siyar da su a kudancin ƙasar don bautar da su da kuma sauya musu addini.

Shi ma shugaban ƙabilar Igbo a Kano ya barranta waɗancan mutane da ke safarar ƙananan yara zuwa kudancin ƙasar, har ma ya ce duk hukuncin da ya dace da su a zartas ba tare da sassauci ba.